logo

HAUSA

An zabi shugaban Najeriya a matsayin sabon shugaban ECOWAS

2023-07-10 11:07:15 CMG Hausa

An gudanar da taron majalisar shugabannin kasashe da gwamnatoci na kungiyar ECOWAS karo na 63 a Guinea Bissau. Inda aka zabi shugaba Bola Tinubu na Najeriya a taron na jiya a matsayin sabon shugaban ECOWAS na tsawon shekara guda.

Shugaba Tinubu ya maye gurbin shugaba Umaro El Mokhtar Sissoco Embalo na Guinea-Bissau, wanda ya karbi mukamin a watan Yulin 2022.

A yayin taron, shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar kasashen na ECOWAS, sun tattauna batutuwan tsaro da siyasa a yankin yammacin Afirka, tare da mai da hankali kan batutuwan siyasa kamar a kasashen Mali, da Guinea, da kuma Burkina Faso. (Ibrahim Yaya)