logo

HAUSA

An gudanar da zanga-zangar adawa da kona Alkur'ani mai tsarki a birnin Stockholm

2023-07-10 10:34:34 CMG Hausa

Dubban dubatar masu zanga-zanga suka taru a tsakiyar birnin Stockholm don nuna adawa da kona Alkur'ani mai tsarki a kasar Sweden.

An gudanar da taron ne a dandalin dake kusa da wani masallaci inda wani mutum ya kona Alkur’ani mai tsarki a ranar 28 ga watan Yuni.

A cewar ’yan sandan Sweden, zanga-zangar ta ranar Lahadi ta samu kusan mahalarta 3,000, kamar yadda jaridar Dagens Nyheter (DN) ta ruwaito.

Mustafa Issa shugaban hadaddiyar kungiyoyin addinin Islama na kasar Sweden wanda ya shirya zanga-zangar ya shaidawa DN cewa kona Alkur'ani mai tsarki kalaman kiyayya ne da bai kamata a bari ba. (Yahaya Babs)