logo

HAUSA

Najeriya za ta gyara tinunan mota da nisansu ya kai kilomita 36,000 a kasar

2023-07-10 14:09:19 CMG Hausa

Nan ba da jimawa ba hukumar dake da alhakin gyaran tituna mallakin gwamnatin tarayyar a Najeriya FERMA za ta fara aiki cike ramukan dake wasu daga cikin manyan titunan kasar.

Mukaddashin manajan-daraktan hukumar Mr. Godson Amos ne ya tabbatar da hakan jiya Lahadi 9 ga wata lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Abuja. Ya ce, saboda yanayin damuna wajibi ne a dukufa wajen yin ciko a titunan da suka farfashe.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban hukumar ta FERMA ya ce yana da matukar mahimmanci ga hukumar ta yi duk mai yiwuwa wajen rage wahalhalun da masu ababen hawa ke cikin karo da su yayin da suke tafiye-tafiye a manyan titunan kasar.

Mr. Godson Amos ya tabbatar da cewa aikin gyaran titunan ba zai dauki hukumar sama da makonni 6, ba tare da kammala shi ba, sabo da tuni an fitar da jerin titunan da suke da matukar bukatar kulawar gaggawa musamamn saboda yanayin damuna.

Mukaddashin manajan daraktan ya bayyana cewa hukumar ta karbi korafe-korafe da dama daga ’yan Najeriya masu bin manyan titunan mota a game da rashin kyawun titunan wanda ke matukar barazana ga rayukan matafiya.

Ko da yake, ya alakanta ci gaba da lalacewar hanyoyin mota a wasu yankunan kasar bisa yawan ruwan sama wanda har wani lokaci ya kan karya gadoji ko ma ya yashe wani bangare na titin.

Ha’ila yau ya ce lodin da ya wuce kima da wasu masu manyan motoci ke yi kari kuma da tsufan da wasu titunan kasar suka yi ya taimaka wajen rashin karkon mayan hanyoyin mota a Najeriya.

Tuni dai shugabannin kungiyoyin direbobin kasar suka fara bayyana ra’ayinsu a game da wannan yunkuri.

Alhaji Bala Isma’il Gwarzo shi ne shugaban kungiyar direbobin motocin haya ta Najeriya reshen jihar Kano, “Samun labarin da muka yi na yunkurin gwamnati na cewa za a ci gaba da aikin gyaran tituna, babu shakka ya faranta mana zukata, musamman idan ka duba tsakanin Lokwaja zuwa Abuja, tsakanin Abuja da Kaduna, titunan sun lalace sosai, yanzu idan ka taso daga Abuja zuwa Kaduna wani wajen sai ka tsaya cik kafin ka samu ka wuce sabo da mutuwar titin, haka yake daga Lokwaja zuwa Abuja, wadannan matsaloli sun dami mutane da dama ba sai lallai direbobi ba.”(Garba Abdullahi Bagwai)