logo

HAUSA

An Yi Kira Da A Gaggauta Samar Da Guraben Ayyukan Yi Yayin Bikin Ranar Dunkulewar Nahiyar Afrika

2023-07-09 15:35:00 CMG Hausa

An yi bikin ranar dunkulewar nahiyar Afrika a ranar Juma’a, inda aka yi kira ga kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Afrika (AU), su gaggauta samar da guraben ayyukan yi, da hada harkokin kudi da fasahohin zamani, ta yadda za a kai ga cimma burin kafa yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar.

Da take jawabi yayin bikin ranar, wanda aka yi a wani bangare na dandanlin samar da guraben ayyukan yi na Afrika a hedkwatar AU dake Addis Ababa na kasar Habasha, mataimakiyar shugaban hukumar AU Monique Nsanzabaganwa, ta bukaci kasashe mambobinn AU su samar da dimbin guraben ayyukan yi ta hanyar inganta masana’antu da fasahohi da zuba jari.

Ta ce, AU za ta samar da dalar Amurka biliyan 100 da zummar samar da kanana da matsakaitan sana’o’i miliyan 10 a fadin nahiyar, a matsayin wani kokari na tabbatar da mata da matasa sun shiga cikin duniyar amfani da fasahohin zamani a hada-hadar kudi, zuwa shekarar 2033.

A nasa bangaren, Hailemariam Desalegn, shugaban kungiyar AeTrade, ta masana da ‘yan kasuwan Afrika dake rajin inganta cinikayya ta yanar gizo a tsakanin kasashen nahiyar, kana tsohon Firaministan Habasha, ya ce kusan matasan Afrika miliyan 3 da suka kammala karatu ne ke samun ayyukan yi a kowace shekara, duk da cewa adadin matasan nahiyar dake kammala karatun a kowace shekara na kai wa miliyan 19.

Ya kuma yi kira da a kara jan hankalin masu zuba jari a nahiyar domin samar da guraben ayyukan yi ga matasa masu neman aiki, wanda ake hasashen adadinsu zai kai miliyan 375 a shekarar 2030. (Fa'iza)