logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya yi tir da luguden wuta a Omdurman na Sudan

2023-07-09 16:05:48 CMG Hausa

 

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da luguden wuta ta sama a birnin Omdurman dake kusa da Khartoum a kasar Sudan, lamarin da ya yi sanadin salwantar rayuka akalla 22.

Cikin wata sanarwa, Antonio Guterres ya ce ya kadu da rahotannin tashin hankali mai tsanani da yadda yake rutsawa da jama’a a fadin Darfur dake yammacin Sudan. Ya kuma bayyana yadda ake take dokokin jin kai da na kare hakkokin jama’a a matsayin abu mai hadari da tayar da hankali.

Ya ce ya damu kwarai ganin yadda rikicin dake gudana a Sudan ke ingiza kasar shiga yakin basasa baki daya, lamarin da ka iya mummunan tasiri a yankin. Ya kuma jaddada kira ga rundunar sojin Sudan da ta RSF, su dakatar da bude wuta, yana mai bukatar su kiyaye nauyin da ya rataya a wuyansu karkashin dokokin jin kai da na kare hakkokin bil Adama na kasa da kasa, domin kare fararen hula.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, MDD za ta ci gaba da yunkuri karkashin kungiyar tarayyar Afrika AU, da nufin kawo karshen rikicin.(Fa'iza)