logo

HAUSA

Sojojin Nijar na FDS na ci gaba da samun nasarori kan ’yan ta’adda

2023-07-09 15:59:42 CMG Hausa

Rundunar sojojin Nijar FAN da ke fagagen daga daban daban kan yaki da ta’addanci da kungiyoyi masu aikata manyan laifuka, na ci gaba da samun nasarori kan abokan gaba masu adawa da zaman lafiya ta hanyar kai samame a wasu yankunan kasar Nijar da ake fama da tashin hankali.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

 

A cikin mujallar “bulletin d’information” ta soja da ta fito kwanan nan ta bada labarai kan ayyukan soja da aka gudanar a cikin kasa, babbar cibiyar bada labaru, da hulda da jama’a ta hadkwatar sojoji ta nuna cewa bayan hadarin fashewar wata nakiya da ta janyo mutuwar sojoji 4 da raunata wasu sojoji 3 na rundunar Niyya, an kakkauta mai da martani ta hanyar kai samame da suka taimaka wajen murkushe kungiyoyin ’yan ta’adda 2 da kama ’yan ta’adda 54 a cikin yankunan Kossa da Gountiyena. Haka kuma dakarun Niyya sun kama ’yan ta’adda 5 a yankin Dolbel, da lalata mota guda da babura 9 da kuma sanya hannu kan bindigogi kirar AK47 guda 5, karamar bindiga 1 da tarin harsasai da abubuwa masu fashewa. A ranar 25 ga watan Yuni, ’yan ta’adda 2 aka kashe a yankin Begorou da lalata baburansu 2, aka kama makamansu, harsasai da kuma kayayyakin soja. Cikin yankin Tillabery, rundunar Almahaou ta gudanar da aikin larwai ta jirage masu saukar angulu da suka taimaka wajen murkushe ’yan ta’adda 3, da kama wani dan ta’adda 1 da aka raunata, da karbe bindigogi kirar AK47 guda 5 da lalata baburan ’yan ta’adda guda 6.

Haka kuma mujallar FAN ta ba da labarin cewa a yankin Agadez inda rundunar Garkoua take gudanar da ayyukan kakkaba, kwanciyar hankali na dawowa sannu a hankali. Amma duk da haka, a yayin wani samame na bincike cikin yankin Tabarkat, an gano wata mabuyar makamai tare da bindigogi 2 kirar AK47 da harsasai da wasu kayayyaki da kama mutum mai hada baki da miyagu. A cewar mujallar, ayyukan mako-mako na sojojin FAN cikin yankin tsaro na 8 na Dirkou sun taimaka wajen masu neman zinariya ta barauniyar hanya 62 da kama na’urorin neman karafe.

A yankin Diffa, a cewar majiyar guda ta sanar da cewa ayyukan dakarun hadin gwiwa da ke sintiri a yankunan N’Guigmi, Baroua da Toumour sun taimaka wajen kama kayayyaki da dama da wasu mutane 2 masu alaka da ’yan ta’addan Boko Haram.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.