logo

HAUSA

Uwargidan shugaban tarayyar Najeriya ta ce al`ummar kasar za su amfana daga fa`idar shirin farfado da rayuwar iyali da ta kirkiro da shi

2023-07-08 16:01:12 CMG Hausa

Mai dakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta tabbatarwa `yan Najeriya cewa zasu samu amfanuwa sosai karkashin shirin da ofishinta ya bullo da shi mai taken farfado da rayuwar iyali da zarar shirin ya fara aiki gadan gadan.

Ta tabbatar da hakan ne jiya juma`a 7 ga wata a ofishinta dake fadar shugaban kasa yayin taro karo na biyu na shugabannin hukumar gudanarwar Shirin.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Uwargidan shugaban kasar wanda itace shugabar Shirin na kasa baki daya tace an rigaya an samar da dukkan matakan da suka kamata domin samun nasarar gudanuwar Shirin a daukacin jahohi kasar 36 har da birnin Abuja.

Ta ce Shirin zai yi naso har zuwa kananan hukumomin kasar, kuma yana dauke da aikace aikace daban daban da suka kunshi aikin gona, kiwon lafiya, ilimi, kyautata rayuwa da kuma samar da abubuwan da za su inganta tattalin arzikin jama`a.

Sanata Oluremi Tinubu ta cigaba da cewa ta shirya gudanar da taro da daukacin matan gwamnoni a ranar 14 ga wannan wata na Yuli, inda a wannan lokaci ne zata sanar da su matakan da ake bukata domin samun nasarar aiwatar da tsare tsaren da Shirin yake kunshe da su.

A nata jawabin yayin taron, uwar gidan mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Shettima wadda ita ce mataimakiyar shugaban Shirin na kasa, bayyana gamsuwar `yan hukumar gudanarwa Shirin ta yi , tare da bukatar cewa lokaci yayi da `yan Najeriya ya kamata su marawa kokarin gwamnatin tarayya a fafutukar da take yi na samar da rayuwa mai sauki ga kowa.

Haka ita ma sakatariyar Shirin na farfado da rayuwar iyali Barr. Chioma Uzodinma cewa ta yi Shirin zai yi kokarin shiga cikin sahun ayyukan hadin gwiwa da sauran sassa domin samar da al`umma mai walwala da cigaba.(Garba Abbdullahi Bagwai)