logo

HAUSA

Sharhi: Sin da Amurka ba su bukatar zama abokan gabar juna

2023-07-08 22:14:53 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Yanzu haka sakatariyar baitulmalin kasar Amurka Janet Yellen na yin ziyarar aiki ta kwanaki hudu a kasar Sin, wadda kuma ta kasance ta biyu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Biden da suka kawo ziyara a kasar Sin, biyo bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya yi a watan da ya gabata. A labarin da aka bayar, an ce, da mista Antony Blinken da Madam Yellen dukkansu sun bayyana cewa, Amurka na son tabbatar da daidaiton da shugabannin kasashen biyu suka cimma a yayin ganawarsu a gefen taron kolin G20, wanda aka gudanar a bara a tsibirin Bali na kasar Indonesia, wato su martaba juna, da zama lafiya da juna, da kuma yi hadin gwiwa ta cin moriyar juna, kuma Amurka ba ta son ganin rarrabuwar kawuna a tsakaninta da kasar Sin.

Amurka ta tura manyan jami’anta zuwa kasar Sin tare da yin kalaman da suka kasance tamkar neman kyautata hulda da kasar Sin, sai dai ba lallai al’amarin haka yake ba, kasancewar bayan da mista Blinken ya koma gida, ya bayyana wa ’yan jarida cewa, “sabanin dake tsakanin Sin da Amurka ba wani boyayyen abu ba ne. Kuma Amurka za ta ci gaba da kare moriyarta da akidunta, haka kuma za ta ci gaba da yin abin da kasar Sin ba ta son gani, tare da furta abubuwan da Sin din ba ta son ji.”

A hakika, sabanin da ke tsakanin Sin da Amurka ya samo asalinsa ne daga irin akidun da kasar ta Amurka ke da shi. A ganin kasar Amurka, moriyarta, da tsaronta, sun fi muhimmanci fiye da na sauran kasashe. Tana kuma yayata irin salon ’yanci da dimokuradiyya, da hakkin dan Adam nata a duniya, ta yadda duk wata kasar da ba ta yi mata biyayya ba, to za ta dauke ta a matsayin abokiyar gaba, har ma za ta yi kokarin dakile ta, da rushe mulkinta, har ma kaddamar da yaki a kanta, kuma irin wannan misali ba ya lasaftuwa.

Kasar Sin a nata bangaren tana daukar matsayi akasin haka, inda ta gabatar da shawarar “raya daukacin kasashen duniya baki daya”, shawarar da ta jaddada muhimmancin rashin barin wata kasa a baya, baya ga kuma shawarar “kiyaye tsaron bai daya na kasashen duniya” da kasar ta gabatar, wadda ta jaddada muhimmancin kiyaye zaman lafiya da tsaro na bai daya na daukacin kasashen duniya. Sai kuma shawarar “raya mabambantan wayewar kai na duniya” da kasar Sin ta gabatar, wadda ta jaddada muhimmancin martaba kasancewar mabambantan wayewar kai a duniya.

Manufofi mabanbanta da Amurka da Sin ke yayatawa, na da nasaba ne da banbancin tunani. Amurka a bangaren ta, na da imanin cewa, idan wani ya samu kudi, hakan na nufin wani zai rasa nasa, yayin da a nata bangare kasar Sin ke ganin mutane da dama, na iya ci daga kwarya guda, sabo da za a iya girka abincin da zai ishi kowa. Bugu da kari, Amurka na ganin ba zai yiwu teku daya ya ishi manyan kasashe biyu wanka ba; A daya bangaren kuma, Sin na ganin wannan duniya ta ishi kowa watayawa, da samun ci gaban bai daya, da wadatar daukacin kasashen duniya, ciki har da Sin da ita kan ta Amurka.

Kafin Madam Yellen ta tashi zuwa kasar Sin, wani dan jarida da ya bi ta a wannan ziyara, ya wallafa wata makala mai taken “Yellen za ta kai ziyara kasar Sin don daidaita dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu” a jaridar “New York Times”, kuma a bangaren ra’ayoyin masu karatu, akwai Amurkawa da suka karanta makalar da suka bayyana cewa, da fatan Yellen za ta bude sabon babi da kasar Sin, sabo da Sin da Amurka ba su bukatar zama abokan gaba ga juna.

Abin haka yake. A hakika, Sin da Amurka sun kasance suna cin moriyar juna a huldarsu ta tattalin arziki, kuma kowanensu ba zai amfana da yakin ciniki ko rarrabuwar kawuna a tsakaninsu ba, kuma abu ne mai kyau kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya su zauna su yi musayar ra’ayi da juna.

Madam Yellen na ci gaba da wannan ziyara a kasar Sin, mu kuma muna zuba ido don gani abin da za ta fada, musamman abin da za ta aikata daga baya.