logo

HAUSA

Kuri’un jin ra’ayi na CGTN: Shirin Japan na zubar da dagwalon nukiliyar ta a Teku ya karfafa damuwar kasashen duniya

2023-07-08 21:44:35 CMG Hausa

Kasar Japan ta nace sai ta juye ruwan dagwalon nukiliyar ta a cikin Teku, tana mai watsi da damuwa, da adawar da sassan kasa da kasa suke nunawa don gane da hakan.

Sakamakon wasu kuri’un jin ra’ayin al’umma guda 2 da kafar CGTN ta gudanar ta yanar gizo sun nuna cewa, kaso 94.85 bisa dari na wadanda suka amsa tambayoyi sun yi Allah wadai da matakin kasar Japan, suna masu bayyana shi a matsayin tsananin rashin sanin ya kamata, kana karin wasu kaso 3.64 bisa dari kwatankwacin na watanni 3 da suka gabata. Yanzu haka dai sassan kasashen duniya na ta kara nuna damuwa ga matakin da Japan din ke burin aiwatarwa.

Wannan bincike, wanda kafar CGTN ta fitar ta tashoshin ta na Turanci, da Faransanci da Larabci, da yarukan Sipaniya da na Rasha, ya samu amsoshi daga mutane kusan 34,000 cikin sa’o’i 24. (Saminu Alhassan)