logo

HAUSA

Afirka ta kudu ta gayyaci jagororin kasashen Afirka zuwa taron kolin kungiyar BRICS dake tafe

2023-07-08 16:53:37 CMG Hausa

Jakadan kasar Afirka a kungiyar BRICS, a sashen lura da alakar kasa da kasa da hadin gwiwa na kasar Afirka ta kudu Sherpa Anil Sooklal, ya ce kasar sa ta gayyaci daukacin jagororin kasashen Afirka zuwa taron kolin kungiyar BRICS dake tafe a watan Agusta.

Sooklal, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana a ranar Alhamis, ya ce shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, na fatan shugabannin Afirka za su yi musayar ra’ayoyi tare da shugabannin kungiyar BRICS, yayin taron kolin kungiyar da zai gudana a birnin Johannesburg.

Jami’in ya kara da cewa, yayin zaman taron, za a maida hankali ga tattauna yadda kasashe mambobin BRICS za su yi hadin gwiwa da kasashen Afirka, wajen cimma nasarar bunkasar tattalin arziki. Ya ce shugaba Ramaphosa, zai shiryawa shugabannin BRICS din liyafa ta musamman, wadda ake fatan shugabannin Afirka za su halarta.

(Saminu Alhassan)