logo

HAUSA

NPC: Shugaban Najeriya Tinubu zai sanar da sabuwar ranar aikin kidaya da yiwa gidaje rijista

2023-07-07 13:54:30 CMG HAUSA

 

Hukumar kidayar jama’a ta kasa a tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa nan bada jimawa ba shugaba Bola Ahmad Tinubu zai sanar da sabuwar ranar da za a gudanar da aikin kidaya da yiwa gidaje rijista na 2023.

Shugaban hukumar Alhaji Nasiru Kwarra ne ya tabbatar da hakan jiya Alhamis lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya gana da shugaban kasa a fadar sa dake birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.