logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin ya yi kira ga Amurka da ta dawo da yarjejeniyar nukiliyar Iran da wuri don bin diddigin lamarin

2023-07-07 13:43:30 CMG HAUSA

 

Geng Shuang, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya yi jawabi a yayin bude taron kwamitin sulhu na MDD kan batun nukiliyar kasar Iran a ranar 6 ga wata, inda ya yi kira ga Amurka da sauran kasashen duniya da suka dace don dawo da cikakken shirin aiki na haɗin gwiwa kan batun nukiliyar Iran.

Geng Shuang ya yi nuni da cewa, yarjejeniyar da aka cimma kan batun nukiliyar kasar Iran wata muhimmiyar nasara ce ta diflomasiyya tsakanin bangarori daban daban da kudurin kwamitin sulhu ya amince da shi. Gwamnatin Amurka da ta shude ba tare da shawarar kowa ba ta fice daga yarjejeniyar da aka cimma, inda ta matsa lamba kan Iran tare da haddasa rikicin nukiliyar Iran. Tun daga watan Afrilun 2021, bangarori daban-daban sun gudanar da shawarwari masu amfani sau da yawa a karkashin hadin gwiwar Tarayyar Turai, wanda ya rage sauran mataki daya daga ci gaba da bin doka. Sai dai abin bakin ciki shi ne, tun watan Agustan shekarar da ta gabata ne tattaunawar ta yi tsami.

Geng Shuang ya ce babban abin da ke gaban dukkan bangarorin shi ne su kara yin kokarin dawo da yin shawarwari cikin sauri. Kasar Sin ta yi kira ga Amurka da ta dage dukkan nau’ikan takunkumin da aka kakkabawa kasar Iran, da dakatar da barazanar yin amfani da karfi, da samar da yanayi mai kyau don fara aiwatar yarjejeniyar. (Yahaya Babs)