logo

HAUSA

Mutane 16 sun mutu a Afirka ta Kudu sakamakon shakar sinadarin Nitrate

2023-07-06 11:06:38 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Afirka ta kudu sun tabbatar da mutuwar mutane 16, sakamakon shakar wani abu da ake zaton iskar gas ne a Boksburg dake gabashin birnin Johannesburg.

Kafafen yada labarai na kasar sun rawaito hukumomin agajin gaggawa na cewa, binciken farko ya nuna cewa, ana iya danganta hakan da hakar zinare ba bisa ka'ida ba da jama’a ke yi a yankin.

Galibi masu hakar zinare ba bisa ka'ida ba, suna amfani da Nitrate oxide don hako zinari daga ramukan hakar ma'adinan da aka yi watsi da su.

Wani jami'in hukumar agajin gaggawa ya bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceto a wurin da lamarin ya faru, yayin da ake fatan gano karin gawarwaki. (Ibrahim Yaya)