Kungiyar SCO ta kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya
2023-07-06 10:39:09 CMG Hausa
Bayan da kasar Iran ta shiga kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a ranar 4 ga wannan wata, adadin kasashe membobin SCO ya karu zuwa 9. Wannan kungiyar da ke mai da hankali kan tsaro, ci gaba da hadin gwiwa, a kullum tana samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Turai da Asiya da duniya baki daya.
A wannan rana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taro na 23 na majalisar gudanarwar kungiyar SCO daga birnin Beijing ta kafar bidiyo tare da gabatar da muhimmin jawabi. Game da ci gaban kungiyar SCO a nan gaba, shugaba Xi ya gabatar da shawarwari mai kunshe da abubuwa guda biyar, wadanda suka hada tsare-tsaren tsaro na duniya, da ayyukan raya kasa, da raya wayewar kai a duniya, da zana taswirar ci gaba mai dorewa ga kungiyar SCO..
A cikin shekaru fiye da 20 bayan kafuwar kungiyar SCO, kungiyar ta hada kan kasashe daga yankuna daban daban, masu al’adu da wayewa daban daban, da tsarin samun bunkasuwa daban daban, da samun nasarar kafa hanyar samun bunkasuwa ta yin shawarwari da hadin gwiwa ba tare da nuna kiyaya ga juna ba. A matsayinta na kasar da ta kafa wannan kungiya, kasar Sin har kullum tana bayar da gudummawa wajen jagoranci da sa kaimi ga ci gaban kungiyar SCO. (Zainab)