logo

HAUSA

Wakilin Sin ya kalubalanci Amurka da Birtaniya da su dakatar da aikin soja ba bisa doka ba a Syria

2023-07-06 11:13:20 CMG Hausa

Wakilin Sin ya yi jawabi game da batun Syria a yayin taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 53 jiya Laraba, inda ya kalubalanci kasashen Amurka da Birtaniya da su dakatar da ayyukan sojan da suke gudanarwa a kasar Syria ba bisa doka ba, yana mai cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali, shi ne babban abin da zai tabbatar da kare hakkin dan Adam, kana inganta sasantawa ta siyasa, ita ce kawai mafita ga batun Syria. Dawowar Syria cikin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa bayan shekaru 12 na nuni da cewa, ita ce burin bai daya na kasashen yankin na kawar da tashin hankali tsakanin rukunoni da neman ci gaba cikin lumana.

A yayin taron, wakilin Sin ya kuma yi tsokaci kan batun Venezuela, inda ya ce, kasar Sin za ta kiyaye kundin tsarin MDD da muhimman ka'idoji da suka shafi huldar kasa da kasa, da mutunta hanyar samun bunkasuwa da al'ummar kasar Venezuela suka zaba da kansu . (Zainab)