logo

HAUSA

Shawarar BRI na samar da sauyi mai muhimmanci a Afrika

2023-07-06 09:57:51 CMG Hausa

Daraktan cibiyar binciken manufofin Afrika ta Kenya, Peter Kagwanja, ya bayyana shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” a matsayin wadda ta sauya Afrika ta wata hanya mai muhimmanci.

Peter Kagwanja ya bayyana hakan ne a baya-bayan nan yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce shawarar ta gabatar da dabarar taimakawa samar da ababen more rayuwa a Afrika, lamarin da ya kai ga samar da ci gaban nahiyar a bangarori da dama. Haka kuma, shawarar ta kunshi dukkan abubuwan da Afrika ke bukata na samun ci gaba mai dorewa.

Da yake bayyana karbar taimakon Sin na gina layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobin Kenya a matsayin misali, Kagwanja ya bayyana cewa Kenya na da tsarin layin dogo mafi inganci a gabashin Afrika. Kuma layin dogon wanda ya mika daga Nairobi har zuwa yankin yammacin kasar, ba inganta saurin tafiya ga jama’a kadai ya yi ba, har ma da rage lokacin da ake bukata na sufurin kayayyaki. Ya ce raguwar lokacin sufurin kayayyaki ya samar da damar samun ci gaban masana’antu da saukaka ci gaban masana’antar samarwa da kere-keren kayayyaki.

A cewar Peter Kagwanja, a baya, ana ganin Afrika a matsayin wadda ke cikin matsi, amma a yanzu, babu wanda ya isa ya ce nahiyar ba ta da makoma. Yana mai cewa, saboda shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, Afrika na farfadowa, inda ya bayyana ta a matsayin mai muhimmanci da kyakkyawar makoma. (Fa’iza Mustapha)