logo

HAUSA

Amsar Xi Jinping ta ba duniya damar fahimtar tsarin binciken hada-hadar kudin na kasar Sin

2023-07-06 15:58:37 CMG Hausa

“A lokacin da na samu labarin cewa shugaba Xi Jinping ya amsa wasikarmu, na yi farin ciki sosai. Bayan na koma gida, zan yi amfani da ilimin binciken hada-hadar kudi da na koya a kasar Sin wajen gina kasarmu.”

A ranar 5 ga wata ne, wata daliba ’yar kasar Malawi, mai karatun digiri na biyu a bangaren nazarin binciken hada-hadar kudi, a jami’ar binciken hada-hadar kudi ta Nanjing, ta bayyana hakan ga wani dan jaridar CMG.

Kwana 1 kafin wanna rana ne, shugaba Xi Jinping ya amsa wasikar da daliban kasashen waje dake karatun digiri na biyu suka aika masa, inda ya karfafa musu gwiwar tuntubar juna da takwarorinsu Sinawa, da fahimtar Sin ta hanyar tsarinta na binciken kudi da kuma bada gudunmawa ga zurfafa abota da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashensu.

A shekarar 2016 ne aka kaddamar da bangaren nazarin tsarin binciken hada-hadar kudi a matakin digiri na biyu, ga daliban kasashen waje a jami’ar, inda zuwa yanzu ya yaye kwararru sama da 280 ga cibiyoyin binciken hada-hadar kudi na kasashe 76 dake kan hanyar siliki.

Ta hanyar karatun, daliban kasashen waje sun kara fahimtar tsarin binciken hada-hadar kudi irin na kasar Sin, da gane jajircewar JKS wajen yaki da cin hanci. Bayan komawa kasashensu kuma, za su zama kashin bayan tafiyar da harkoki da ma kasuwanci a bangaren binciken hada-hadar kudi, tare da bayar da gudunmawa ga ci gaban bangaren. (Faeza Mustapha)