logo

HAUSA

UN: Najeriya ta kasance kasa ta uku a duniya da ake samun yawaitar mace-macen mata masu juna biyu

2023-07-06 10:15:51 CMG Hausa

Asusun lura da yawan al’umma na Majalissar Dinkin Duniya ya ce mata a Najeriya suna cin karo da matsaloli da dama da suke takaita hasken rayukansu .

Wakiliyar asusun a Najeriya Mrs. Ulla Mueller ce ta tabbatar da hakan jiya Laraba 5 ga wata a birnin Abuja cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai wadda take dauke da sa hannun mai magana da yawunta Mal. Kori Habib a shirye-shiryen fara bikin ranar yawan al’umma ta duniya na 2023.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Madam Ulla Mueller ta ce baya ga batun matsalolin haihuwa dake salwantar da rayuwar matan, haka kuma batun cin zarafin mata dake da nasaba da wariyar jinsi da rashin daidaito wajen amfanuwa da tattalin arzikin kasa na daga cikin abubuwan dake haifar da tawayar rayuwa ga ’ya’ya mata a Najeriya.

Wakiliyar asusun lura da yawan al’ummar ta majalissar dinkin duniya ta ci gaba da cewa Najeriya a matsayinta na kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika, sannan kuma daya daga cikin kasashe masu karfin arziki a nahiyar, amma har yanzu an gaza shawo kan matsalolin mace-macen mata masu juna biyu a kasar, wannan ce ta sanya ma a yanzu kasar ke cikin jerin kasashe uku da aka fi samun wannan matsala.

Ta ce ya zama wajibi ne ga asusun ya tabbatar da ganin kowane jinsi na al’umma ana ba shi hakkin da ya kamace shi domin dai ganin al’ummar duniya ta ci gaba da habaka cikin wadata da kuma koshin lafiya.

To kome likitoci a Najeriya za su ce game da wannan rahoto na majalissar dinkin duniya? Dr. Isa Sadiq, babban likita ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, “Maganar mace-macen mata masu juna biyu wajen haihuwa ko kuma bayan haihuwa ba da dadewa ba, babbar mastala ce da ta dade tana addabar kasarmu ta Najeriya. Yana da kyau gwamnati ta samar da manufofi da dokoki wadanda za su taimaka mata su samu haihuwa cikin sauki, akwai bukatar giggina asibitoci bayan an gina sannan kuma a saka kayan aiki wadatattu da kuma ma’aikata da dama domin samun nasarar cetar rayukan mata, sannan kuma a rinka wayar da kan mazaje su rinka taimakawa mata idan suna da juna biyu, haka kuma kungiyoyi kamar na mata ungozomomi da sauran masu sa kai su rinka taimakawa ma’aikatan asibiti domin a taimakawa rage yawa matan dake yawan mutuwa.”

Kididdigar hukumomin lafiya a Najeriya ya nuna cewa kusan mata dubu 50 a kowace shekara ake asarar rayukansu a Najeriya wajen haihuwa. (Garba Abdullahi Bagwai)