logo

HAUSA

Mutum biyu suka mutu kana wasu suka ji rauni a gobarar da ta tashi a kamfanin SONIDEP da ke birnin Zinder

2023-07-06 09:32:30 CMG Hausa

A birnin Zinder, birni na biyu mafi girma a kasar Nijar, wata gobara ta tashi a ranar jiya Labara 5 da rana ga watan Julin shekarar 2023 a wani wurin ajiyar man fetur na kamfanin kayayyakin man fetur na kasa SONIDEP.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya turo mana da rahoto kan wannan gobara.

A cikin wannan gobara da ta tashi ba zata, mutum biyu aka tabbatar da sun mutu, wani direban mota da karan motarsa, yayin da wasu suka ji rauni. Haka kuma motocin dakon man fetur biyu gobarar ta lakume. A cewar wasu ganau da lamarin ya faru gaban idonsu. Sun bayyana cewa wutar ta tashi ne a daidai lokacin da motocin dakon man fetur biyu din suke nan suna zubar man fetur din nasu cikin manyan kibunan ajiyar man fetur na kamfanin SONIDEP da ke birnin na Zinder. Sai dai, Allah ya takaita wannan barna, ganin cewa wadannan kibuna ajiyar man fetur din sun tanadi abubuwan sanyi domin kashe gobara, dalilin da gobarar ta kiyaye su, a cewar shugabannin wannan SONIDEP da ke wurin. Bayan samun labari, hukumomin wurin a karkashin jagorancin gwamnan Zinder da sun je wurin da gobarar ta tashi domin jajantawa da kawo goyon bayansu ga wadanda suka taimaka wajen kashe gobarar.

Wannan gobara ta janyo rudani da fargaba a cikin zukatan mazauna unguwar da wannan gobara ta tashi, duk da cewa jami’an tsaro sun killace yankin domin bada kariya ga mutane. Wannan gobara da ba irinta ba ce ta farko ta sake janyo ce ce kuce da aza ayar tambaya kan matsalar tsaron wuraren ajiyar man fetur na kamfanin SONIDEP da ke sauran yankunan kasa, musammun ma da ke cikin manyan biranen kasar kamar wannan gobara da ta tashi a birnin Zinder. A halin yanzu, masu bincike sun fara aiki domin gano musabbabin abkuwar wannan gobara da ’yan kwana-kwana suka kwashe tsawon sa’o’i kafin su kawo karshenta.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.