logo

HAUSA

Shugaban kasar Nijar ya gana da babban kwamishinan MDD game da ‘yan gudun hijira

2023-07-06 11:08:41 CMG Hausa

Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya gana a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai da babban kwamishinan MDD game da ’yan gudun hijira, mista Filippo Grandi dake wata ziyarar aiki a Nijar tun ranar Talata, 4 ga watan Yulin shekarar 2023.

Daga birnin Yamai, wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Daga fitowarsa daga wannan ganawa, babban kwamishinan MDD game da ’yan gudun hijira, mista Filippo Grandi ya shaidawa manema labarai cewa tattaunawa tare da shugaban kasar Nijar ta rataya ne kacokan kan matsalar ’yan gudun hijira a Nijar da shiyyar yammacin Afrika. Game da wannan matsala, jami’in na MDD ya jaddada cewa shugaba Mohamed Bazoum ya bayyana kalubale da dama da shiyyar take fuskanta musamman ma kasashe makwabta dake fama da matsalar tsaro mai girma kamar kasashen Mali da Burkina Faso. Hakan kuma na tattare da matsalolin jin kai da kuma matsin lamba na hijirar al’umomi zuwa kasar Nijar. A game da wannan, babban kwamishinan MDD game da ’yan gudun hijira ya sanar da cewa Nijar na karbar kusan ’yan gudun hijira dubu 300 da suka fito daga kasashen Mali, Burkina Faso, Nijeriya da kuma wasu kasashe. A nan, mista Filippo Grandi ya yi imani cewa ta dalilin wadannan tashe-tashen hankali, kasar Nijar na fuskantar matsalar kaurar mutane na cikin gida, wannan kuma muhimmin kalubale ne, in ji jami’in na MDD. Daga karshe mista Filippo Grandi ya yabawa Nijar, wanda duk da sauran kalubale da matsalolin tattalin arziki da na jama’a, da matsin lambar karuwar al’umma na ci gaba da kasancewa kasa mai karbar baki da hannu biyu-biyu. Kuma mista Filippo ya tabbatar wa shugaban kasar Nijar cewa kungiyar kula da ’yan gudun hijira ta MDD za ta ci gaba da tallafawa kasar Nijar a wannan fanni.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.