logo

HAUSA

Matsalar karancin ruwan sha yana ci gaba da jefa mazauna garin Gusau cikin kuncin rayuwa

2023-07-05 09:20:56 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Zamfara ta sha alwashin kawo karshen matsananin karancin ruwan sha da mazauna garin Gusau, fadar gwamnatin jihar suka shafe sama da shekara suna fuskanta.

Gwamnan jihar Dauda Lawal ne ya tabbatar da hakan jiya Talata lokacin da yake  kaddamar da wani kwamiti da zai yi aikin duba yadda za’a magance matsalar ruwan sha wanda ya kawo cikas ga yanayin walwala da zamantakewar al’ummar yankin.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Mazauna birnin suna rayuwa cikin kunchi sakamakon daukar lokaci da suka yi suna cikin matsalar karancin ruwan sha da na amfani yau da kullum.

“Ina kira ga shugabanni don Allah, su ji tsoron Allah, su taimakawa talakawa, walalhi mu talakawa muna cikin halin kaka-nika-yi, yanzu na tashi ba ni da abincin da zan ci, ba ni da ruwan da zan baiwa diyya ta ko kuma na dafa abinci ko kuma na yi alwala domin na yi ibada kuma shi ma miji na ba shi da shi.”

“Babu ruwa muna sayen jarga naira dari-dari kuma wani lokaci ma sai ka nemi ruwan gaba daya ka rasa musamman a wajen hayin asibitin Shagari, wani lokaci kona tsarki bama samu balle na alwala”.

“Don Allah a taimaka mana a ba mu ruwan sha, a yi mana borehole-borehole a saka mana sololi muna da matsalar ruwa, matsalar ruwa ta yi yawa a garin Gusau.”

Sakamakon ci gaba da koke-koken mazauna garin na Gusau ya sanya a jiya Talata gwamnan jihar ta Zmafara ya kaddamar da kwamiti mai wakilai 9 da za su nazarci hanyoyin da za a warware wannan matsala da ta ki ci ta ki cinyewa.

Kwamitin na karkashin jagorancin tsohon babban sakatare a ma’aikatar albarkatun ruwa injiniya Sani Bawa Dauran.

Gwamnan ya baiwa kwamitin wa’adin makonni biyu domin ya gabatar da rahotonsa ta yadda gwamnati za ta fara aiki warware matsalolin cikin gaggawa.

Sai dai gwmanan ya ja hankalin ’yan kwamatin kamar haka, “Na yi imanin ba za ku ci amanar gwamanti ba, ba kuma za ku ci amanar al’umma ba, wanann abu ne na yi shi har ga Allah kuma na ba ku amanar al’umma. In kunchi amanar al’ummar ku da Allah, in kuma kun yi abu mai kyau to kun san sakamako.”

Karancin ruwan sha a garin Gusau ya sanya da yawa yara ba sa zuwa makaranta saboda debowa iyayen su ruwa a wani rafi dake wajen garin Gusau, wanda a kwanakin baya yara sama da 8 suka rasa rayukan su bayan da wani kwale kwale ya nitse da su lokacin da suke kokarin debo ruwan sha a tsakiyar kogi. (Garba Abdullahi Bagwai)