logo

HAUSA

MDD: Yawan mutanen dake shiga Habasha daga Sudan ya kusa kaiwa dubu 60

2023-07-05 10:31:00 CMG Hausa

Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD ko UNOCHA a takaice, ya sanar da cewa, adadin mutanen dake shiga kasar Habasha daga Sudan, ya kai kusan dubu 60.

A cewar rahoton na UNOCHA, babu alamun lafawar shigar da jama'a ke yi cikin kasar Habasha daga Sudan da ke fama da rikici, inda sama da kashi 75 cikin 100 na wadanda suka isa kasar cikin makonni biyun da suka gabata, 'yan kasar Sudan ne.

A ranar 15 ga watan Afrilu ne, kazamin fada ya barke a Khartoum, babban birnin kasar ta Sudan, inda nan da nan ya bazu zuwa sassa daban-daban na kasar. (Ibrahim Yaya)