logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su mai da hankali kan ruwan dagwalon nukiliyar da Japan za ta zubar a cikin teku

2023-07-05 09:59:29 CMG Hausa

Kasar Sin ta yi kira ga kasa da kasa, da su sanya ido sosai kan yadda kasar Japan za ta zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, inda ta yi gargadin cewa, hakan na iya haifar da babbar matsala ga muhallin tekun duniya, da lafiya, da ma matsugunan jama'a.

Da yake gabatar da jawabi a yayin taron majalisar kare hakkin dan-Adam ta MDD karo na 53 dake gudana yanzu haka, jami'in diflomasiyyar kasar Sin ya yi nuni da cewa, zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku, daidai yake da dawo da hadarin illar nukiliya ga daukacin bil-Adama.

Jami'in diflomasiyyar na kasar Sin ya shaidawa majalisar cewa, matakin da kasar Japan ta dauka ya saba wa muradun da'a na kasa da kasa, da dokokin kasa da kasa kamar yarjejeniyar MDD kan dokar teku, da yarjejeniyar London ta hana gurbatar ruwa ta hanyar zubar da sharar gida da sauran al'amura.

A cewarsa, kasar Sin tana sake yin kira ga Japan, da ta dakatar da shirinta na zubar da ruwan dagwalon a cikin teku, maimakon haka ta sarrafa shi ta hanyar kimiyya, aminci da gaskiya, ta kuma hada kai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, don aiwatar da matakan da suka dace game da tsarin sa ido na kasa da kasa na dogon lokaci, wanda zai shafi makwabtan Japan da sauran masu ruwa da tsaki ba tare da bata lokaci ba. (Ibrahim)