logo

HAUSA

Kasar Sin da Morocco sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya don bunkasa hadin gwiwa a fannin noma

2023-07-05 10:43:10 CMG Hausa

A jiya Talata ne, kasashen Sin da Morocco suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna domin inganta hadin gwiwa a fannin aikin gona.

Ministan noma da karkara na kasar Sin Tang Renjian ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, tare da Mohamed Sadiki, ministan aikin gona, kamun kifi, raya karkara, ruwa da gandun daji na Morocco.

A cikin yarjejeniyar fahimtar junar da suka kulla a birnin Rabat, hedkwatar kasar Morocco, kasashen biyu sun amince da kara yin hadin gwiwa a fannonin kamun kifi, da fasahar sarrafa kayayyakin ruwa, da kiwo, da daidaita fasahar noma zuwa ta zamani, da dabarun ban ruwa, da sarrafa ruwa.

Tang ya yaba da kyakkyawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Morocco a fannonin noman kayan lambu iri-iri, da fasahar noma, bincike da raya magungunan dabbobi da rigakafi, yayin da kasashen biyu ke da kamanceceniya a fannin aikin gona. (Yahaya)