logo

HAUSA

Daliban harshen Sinanci a Ghana sun dawo da bikin da suka saba yi a kowace shekara bayan da suka dakatar a dalilin COVID-19

2023-07-04 10:20:53 CMG Hausa

Daliban da ke koyon harshen Sinanci a jami'ar Ghana sun dawo da bikin mako da suka saba yi a kowace shekara a bayan dakatarwa na tsawon shekaru uku a dalilin cutar COVID-19.

A yayin kaddamar da bikin, shugabar kungiyar daliban da ke koyon harshen Sinanci ta jami'ar Ghana Herbert Appiatu Danquah, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, bikin wanda ya cika shekaru 14 da kafuwa, zai ci gaba da ba da gudummawa wajen zurfafa huldar al'adu tsakanin Ghana da Sin, tare da kara ingiza sha'awar ’yan Ghana wajen koyon harshen Sinanci.

Danquah ya ce, ayyukan da za a yi na tsawon mako guda, za su hada da gayyato tsofaffin daliban harshen Sinanci, da kwararru kan huldar dake tsakanin Sin da Afirka, da kuma daidaikun mutanen da suka yi aiki tare da ’yan uwa Sinawa su gabatar da jawabi ga daliban kan dangantakar Ghana da Sin.

Prince Akantogdaam, tsohon shugaban kungiyar, ya ce ya yi farin ciki da dawowar bikin a jami'ar, ya kara da cewa sha'awar daliban Sinanci ya karu cikin ’yan shekarun nan. (Yahaya)