logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Gombe ta kaddamar da shirin amfani da motocin haya wajen dauko mata masu juna biyu zuwa asibiti daga kauyuka

2023-07-04 13:53:48 CMG Hausa

Yayin da ake ci gaba da samun karuwar mace-macen mata masu juna biyu a jihar Gombe, hukumar lafiya matakin farko ta jihar PHC ta kaddamar da shirin hadin gwiwa da masu motocin haya dake yankunan karkara domin dauko mata masu juna biyu zuwa asibiti mafi kusa a duk lokacin da bukatar  gaggawa ta tasowa matan.

A lokacin da take zantawa da manema labarai jiya Litinin, Dr. Maryam Abubakar, babbar darakta dake kula da lafiyar iyali ta hukumar, ta ce matsalolin sufuri na daya daga cikin manyan kalubalen da mata masu juna biyu dake yankunan karkara ke fuskanta wajen zuwa asibiti idan sun fara nakuda.

Dr. Maryam Abubakar ta ce shirin hadin gwiwar za a fara gwajinsa ne daga kananan hukumomi guda 5 dake jihar.

Ta ce kafin zartar da wannan shawara sai da masu ruwa da tsaki suka nazarci kananan hukumomin da aka fi samun matsalolin mutuwar mata masu juna biyu dake jihar, inda aka gano cewa babu motocin jigilar marasa lafiya a kananan cibiyoyin lafiya dake kauyukan kananan hukumomin, sannan kuma ba kowacce rana ce ake samun motocin dake zurga-zurga a irin wadannan garuruwa ba.



Daraktan lura da lafiyar iyali ta jihar Gombe ta ce babu shakka wannan shiri zai taimaka sosai wajen dakile mutuwar mata da jarirai a jihar baki daya.

Dr Maryam Abubaakr ta ci gaba da bayani kamar haka, “Makasudin samar da wannan shiri shi ne muna duba mata masu rauni da yake mace mai ciki wani lokaci sai ka ga ta samu zubar jinni bayan haihuwa ko kuma tana nakuda mai gidan ta baya nan babu wanda zai kai ta asibiti da gaggawa, tun da an san nakuda tana bukatar zuwa asibiti da gaggawa don ta samu kula, shi ya sa muka ce masu motocin haya dake cikin kananan hukumomin da muka zaba za su iya kai matan da ’ya’yan su asibiti in dai har matan suka samu tangarda wajen haihuwa, daman mace-macen matan ya kan faru sau tari a lokacin da  mace ta fara zubar da jinni bayan haihuwa ko doguwar nakuda, kuma rashin samun abin hawa a irin wadannan kauyuka zuwa asibiti shi ne babban tashin hankali, wani lokacin kuma irin wadannan mata suna korafin rashin samun mazajensu a duk lokacin da suka shiga irin wannan hali, ko kuma idan ma maigidan yana nan, a makwaftansu babu mai abin hawa da zai iya taimakawa ya kai su asibiti, amma yanzu samun hadin gwiwa da muka yi da wadannan direbobi za mu samar da lambobin wayar kowanne direba ga al’umomin kawai sai dai su kira direban dake yankinsu, shi kuma zai fito cikin gaggawa domin kai matan asibitin dake daf da su.”

Dr Maryam Abubakar a saboda haka ta yi kira ga al’umma da su baiwa shirin cikakken hadin kai da goyon baya domin cimma burin da aka sanya a gaba na rage yawaitar mace-macen mata masu juna biyu a jihar ta Gombe. (Garba Abdullahi Bagwai)