logo

HAUSA

Kungiyar kasashen gabashin Afrika ta kaddamar da shirin "Train Mission" domin bunkasa muyasa tsakanin jama'a

2023-07-04 10:45:50 CMG Hausa

Kungiyar raya kasashen gabashin Afrika IGAD, ta kaddamar da wani shiri na musamma domin bunkasa musaya tsakanin mutanen Habasha da Djibouti.

Shirin wanda IGAD ta yi wa lakabi da "Train Mission for Regional Collaboration", wato manufar jirgin kasa domin hada kan yanki, na hadin gwiwa ne tsakanin Habasha da Djibouti karkashin shugabancin kungiyar IGAD. Shirin wani muhimmin mataki ne na inganta dunkulewar yankin da karfafa abota da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Sakataren zartarwa na kungiyar IGAD Workneh Gebeyehu, ya bayyana yayin bikin kaddamar da shirin a ranar Lahadi cewa, Habasha na hade da Djibouti ta bangaren kasa, kuma ta dade tana dogaro da tashoshin ruwan Djibouti wajen shiga da fitar da kayayyakinta, inda kimanin kaso 95 na harkokin cinikayyarta ke ratsawa ta muhimman hanyoyin Djibouti.

Ya ce hadewar kasashen biyu ta fuskar muhimman ababen more rayuwa kamar sufuri, da sadarwa, da cinikayya, da zuba jari, da tsaro, da lantarki, da albarkatun ruwa, sun kara karfafa alakarsu. (Fa’iza)