logo

HAUSA

Ko me manufar Argentina ta fara biyan bashin waje da kudin Sin RMB ke nufi?

2023-07-03 22:07:33 CMG Hausa

A ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata ne kasar Argentina, ta yi amfani da damarta ta asusun lamuni na duniya IMF, wadda ta tanadi biyan bashi a tsarin musamman na SDR, da amfani da kudin Sin RMB wajen biyan bashin kasashen wajen da IMF ke bin ta, wadanda suka kai dalar Amurka biliyan 2.7.

Wannan ne karon farko da Argentina ta yi amfani da kudin Sin RMB wajen biyan bashin waje. Kaza lika a jajiberin ranar, babban bankin kasar ya sanar da sanya kudin din RMB cikin jerin kudaden da zai rika ta’ammali da su, tare da ajiyar su cikin tsarin hada hadar kudaden kasar, kana ya amince cibiyoyin hada hadar kudi na kasar su bude asusun ajiya na RMB.

Game da hakan, shugaban babban bankin kasar Miguel Ángel Pesce, ya ce kamar sauran kasashen duniya, Argentina ta jima da yin imani ga makomar hada hadar kudi ta kasa da kasa ta amfani da kudin na kasar Sin.  

Argentina ta dade tana fama da matsalar bashin kasashen waje, wanda ke da nasaba da karfin dalar Amurka. A matsayin ta na kasa ta uku mafi karfin tattalin arziki a Latin Amurka, matakin da Argentina ta dauka ya zama wani abun misali. Don kuwa a halin yanzu, bisa kokarin Brazil, da Argentina da wasu kasashe, sauran kasashen yankin Latin Amurka sun gabatar da tunaninsu na “cire tasirin dala”.

Game da hakan, shugaban Venezuela Nicolás MADURO Moros ya bayyana cewa, kamata ya yi a fara gudanar da aikin kawar da babban karfin dala. Kaza lika shi ma shugaban Bolivia Luis Alberto Arce Catacora, ya ce za a tattauna yiwuwar yin amfani da RMB yayin gudanar da cinikayya. Duk wadannan sun bayyana burin kasashe masu tasowa masu yawa, wajen cimma bambancin harkar kudade, da kuma daukar hanyar ci gaba mai zaman kanta. (Saminu Alhassan, Safiyah Ma)