logo

HAUSA

An sake zabar Qu Dongyu a matsayin darekta-janar na FAO

2023-07-03 10:34:23 CMG HAUSA

 

A jiya Lahadi ne aka sake zaben Qu Dongyu a matsayin darekta-janar na Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) a yayin da ake ci gaba da zama karo na 43 na taron FAO.

An fara zaben Qu ne a watan Yunin 2019 domin ya jagoranci hukumar ta MDD kuma shi ne dan kasar Sin na farko da ya taba rike wannan mukamin.

Tun lokacin da ya hau kan karagar mulki, Qu ya jagoranci hukumar ta FAO da himma wajen magance kalubalen da suka shafi samar da abinci a duniya da kuma ba da gudummawa ga ci gaban abinci da noma na dukkan kasashe, musamman kasashe masu tasowa. Kokarin nasa ya samu karɓuwa daga kasashe membobin FAO.

FAO hukuma ce ta musamman ta MDD wacce aka kafa a shekara ta 1945 tare da hedkwata a Roma, kasar Italiya, wacce ke jagorantar hadin gwiwa a fannin abinci da noma. Hukumar tana taka muhimmiyar rawa wajen musayar manufofin abinci da noma na duniya, da daidaita tsare-tsare, da tattara bayanai da ƙididdiga. (Yahaya)