logo

HAUSA

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Faransa ta yi imanin cewa tarzoma da tashe-tashen hankula da suka barke a kasar sun lafa

2023-07-03 10:37:21 CMG Hausa

Da alamun, har yanzu tarzomar da aka kwashe kwanaki ana yi a kasar Faransa ba ta kai ga lafawa ba. Sai dai ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta sanar a jiya da safe cewa, 'yan sanda sun yi nasarar damke sama da mutane 700 a wurare daban-daban da ake gudanar da tarzomar, wanda ya ragu idan aka kwatanta da kwanaki biyu da suka gabata.

Bayanai na cewa, adadin motoci da gine-ginen da aka lalata sun kara nuna raguwar yanayin, kuma munin tashin hankalin ya dan lafa. Gwamnati ta danganta wannan nasara da jami’an ‘yan sanda masu yawa da aka tura.

A halin yanzu tarzomar da ta barke a kasar Faransa, ta bazu zuwa kasashe makwabta. A cewar rahotannin da kafafen yada labarai na kasar Switzerland suka ruwaito a jiya, tarzoma ta barke a yammacin ranar 1 ga wata a birnin Lausanne na kasar Switzerland, inda mutane kusan 100 suka tunzura sakamakon bayanan da aka wallafa a yanar gizo, tare da kai hari kan shaguna da ma 'yan sanda. Rahotanni na cewa, 'yan sandan sun yi nasarar kama mutane 7, 6 daga cikinsu matasa ne.(Ibrahim)