logo

HAUSA

MDD da AU sun yaba wa sojojin Burundi da suka tabbatar da tsaron Somaliya

2023-07-03 10:07:50 CMG HAUSA

 

Wakilan Tarayyar Afirka da na Majalisar Dinkin Duniya a Somalia sun yabawa dakarun wanzar da zaman lafiya na Burundi bisa gagarumin kokarin da suke yi na tabbatar da zaman lafiya a kasar Somaliya.

Mohammed El-Amine Souef, wakilin musamman na shugaban hukumar AU a Somaliya kuma shugabar tawagar wanzar da zaman lafiya ta AU a Somaliya (ATMIS), da Anita Kiki Gbeho, mataimakiyar wakilin babban magatakardar MDD kan shirin ba da taimako na MDD a Somaliya, sun yi bayani kan muhimman gudummawar da Burundi ke bayarwa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka, musamman a Somaliya da Afrika ta Tsakiya.

Souef ya ce Burundi ta ba da gudummawa sosai wajen samar da ingantaccen zaman lafiya ta gama gari musamman ta hanyoyin siyasa da ke mayar da hankali a kan sassantawa da kuma ci gaba da yin hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya da tsaro, a cewar wata sanarwa da ATMIS ta ranar Lahadi ta fitar a Mogadishu, babban birnin Somaliya.

Gbeho ya kuma yaba wa dakarun wanzar da zaman lafiya na Burundi bisa jajircewa da sadaukarwar da suka yi, ya kuma yi alkawarin MDD zai ci gaba da tallafawa tawagar ta AU. (Yahaya)