logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta nuna bakin ciki ga asarar rayukan mutane da dama sakamakon mummunan hadarin mota a Kenya

2023-07-03 21:06:49 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya bayyana matukar bakin ciki ga rasuwar mutane da dama, sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya faru a arewa maso yammacin kasar Kenya.

Bisa rahoton da aka bayar, a ranar 30 ga watan Yuni, wani hadarin mota mai tsanani ya faru a garin Kerry Joe dake arewa maso yammacin Kenya, wanda ya haddasa rasuwar a kalla mutane 52, tare da jikkatar karin wasu mutanen 32.   (Safiyah Ma)