logo

HAUSA

Ruwa da iska mai karfi sun lalata muhallin magidanta kusan sama da 200 a jihar Kebbi

2023-07-03 08:56:27 CMG HAUSA

 

Magidanta fiye da 200 aka yi hasashen sun rasa muhallan su sanadiyar ruwan sama da iska mai karfi a kauyen Zauro dake yankin karamar hukumar Mulki ta birnin Kebbi dake jihar Kebbi a arewacin Najeriya.

Al’amarin ya faru ne a karshen makon jiya cikin dare lamarin da ya sanya iyalai da dama kwanan zaune sakamakon rashin makwaci.

Daga tarayyar Najeriya Wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.