logo

HAUSA

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya ya nemi hadin kan sarakunan shiyyar arewacin kasar wajen shawo kan matsalolin tsaro

2023-07-02 15:50:05 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya yi kira ga shugabannin al`umomin arewa maso yammacin kasar da su hada kai wajen baiwa gwamnati hadin kan da ya kamata a kokarin da take yi na shawo kan matsalolin tsaro da sauran kalubalen dake damun kasar.

Ya bukaci hakan ne a fadar mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa`ad Abubakar dake Sokoto yayin ziyarar barka da salla da ya kai masa .

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. /////

Mataimakin shugaban kasar yace lokaci ya yi da ya kamata ra`ayoyin shugabanni su zo daya wajen samar da dauwamammen zaman lafiya a kasar, ya ce zaman lafiya shi ne tushen da zai tabbatar da ginuwar kowacce kasa a duniya.

Sanata Kashim Shettima ya cigaba da cewa yanzu haka babu taimakon da shugaba Tinubu ke nema wajen `yan Najeriya illa samun goyon bayan su tare kuma da nuna kishin kasa,wanda wannan ce zata kara masa kwarin gwiwar aiwatar da ayyukan da za su tabbatar da kyautatuwar yanayin rayuwar `yan Najeriya a duk inda suke.

Mataimakin shugaban kasar ya ce ya je garin na Sokoto domin gabatar da sakon salla ga mai alfarma sarkin musulmi a madadin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya tabbatar da cewa shugaban kasa yana sane da kalubalen da al`ummomin arewa maso yammacin Najeriya ke fuskanta, musamman a kan batun tsaro, kuma yanzu haka gwamnati tayi nisa wajen kawo karshen lamarin gaba dayan sa.

“A gidan gwamnati na yi dan takaitaccen bayani, arewa muna cikin matsala, ga rashin zaman lafiya ga talauci,ya cancanta mu hada kai, shi ne na yi kira ga gwamna da ya mutunta sarki su kuma hada kai, abin da hadin kai bai yi mana ba rashin hadin kai ba zai taba yi mana ba, ina godiya ga mai alfarma sarki, da gwamna da daukacin al`ummar garin Sokoto”.

A jawabin sa mai alfarma sarki musulmi Alhaji Sa`ad Abubakar godiya ya yi bisa wanann ziyara ta baka da salla da mataimakin shugaban kasar ya kawo masa.

“Yanzu ba lokaci ne na dogaye maganganu ba ne, wannan gaisuwa ce ta barka da sallah kuma muna mutunta zumunci dake tsakanin mu mai girma mataimakin shugaban kasa, muna baiwa gwamnatin tarayyar tabbacin samun hadin kai wajen hidimar da kuke yiwa musulmi da sarakunan dake kasar nan insha Allah zamu cigaba da ba ku cikakken goyon baya domin a samu cigaba da kuma zaman lafiya a kasa baki daya”

Haka kuma mai alfarma Sarkin Musulmin ya kuma yaba da kokarin gwamnati bisa irin managartan matakan data fara dauka wadanda zasu taimaka wajen rage wahalhalun da al`ummar kasa ke fuskanta.(Garba Abdullahi Bagwai)