logo

HAUSA

Jimillar yarjeniyoyi da bangarori daban daban suka daddale yayin taron baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da kasashen Afirka ta kai 120

2023-07-02 21:44:10 CMG Hausa

An rufe taron baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da kasashen Afirka karo na uku a yau Lahadi a birnin Changsha. Yayin taron na wannan karo, bangarori daban daban sun riga suka sanya hannu a kan yarjeniyoyi 120, wadanda darajar kudin su ta kai dalar biliyan 10.3, kuma jimilar kudaden cinikayya da aka cimma a yayin baje kolin ta kai dala miliyan 400.

Daga ranar 29 ga watan Yuni zuwa yau Lahadi ne aka gudanar da taron baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da kasashen Afirka karo na uku a birnin Changsha dake lardin Hunan. Yayin bikin an kuma fitar da ayyukan hadin gwiwa guda 99, wadanda yawan kudinsu ya kai dalar biliyan 8.7, kuma a ciki kasashen Afirka mahalarta, 11 sun shiga yarjeniyoyin hadin gwiwa 74, adadin da ya haura wanda aka gudanar a bikin da ya gabaci. 

Kaza lika an fitar da sakamakon yarjeniyoyin hadin gwiwa guda 34, kuma karo na farko ne aka fitar da ma'aunin cinikayyar Sin da Afirka, tare da kara fitar da rahoto kan dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya.  (Safiyah Ma)