logo

HAUSA

Kasar Faransa tana ci gaba da girke karin ‘yan sanda don tinkarar rikici

2023-07-02 16:39:55 CMG Hausa

Ministan cikin gidan kasar Faransa Gerald Darmanin, ya sanar a jiya Asabar cewa, an tura karin ‘yan sanda da sojoji dubu 45, zuwa sassan kasar domin tabbatar da tsaron. Kaza lika shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sanar a jiyan cewa, bisa la’akari da yanayin kasar, ya dage ziyarar aiki da zai kai Jamus, wadda aka shirya zai fara a yau Lahadi.

Yayin zantawar sa da kafofin watsa labarai, mista Darmanin ya ce ban da kara karfin ‘yan sanda a duk fadin kasar, ma’aikatar cikin gida, ta kuma kara tura ‘yan sanda na musamman, da motoci masu sulke, da jiragen sama masu saukar ungulu, da sauran matakai. Ya kara da cewa, tun daga daren ranar Juma’a zuwa safiyar jiya Asabar, ‘yan sandan kasar sun kama mutane fiye da dubu 1.3, ciki har da mutane 406 da aka kama a birnin Paris babban birnin kasar. (Safiyah Ma)