logo

HAUSA

Sin ta yi kira a mai da hankali kan hakkin mata tsofaffi

2023-07-01 16:03:00 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva Chen Xu ya gabatar da wani jawabi game da mata tsofaffi a madadin kasashe 60 wadanda suka hada da Indiya da Rasha da Saudiyya da Uruguay da Habasha da sauransu a yayin taro karo na 53 na hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar, inda ya yi nuni da cewa, tun bayan da aka kira babban taron mata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, an samu ci gaba a bayyane wajen kare hakkin mata a fadin duniya, amma yanzu adadin mata tsofaffi na karuwa a kai a kai, kuma suna fama da matsaloli iri daban daban, don haka ya dace a kara mai da hankali kan batun game da yadda ake ingiza da kuma kiyaye hakkinsu.

Jami’in ya kara da cewa, bana aka cika shekaru 75 da zartas da “Sanarwar kare hakkin dan Adam ta duniya”, ya kamata bangarori daban daban su dauki hakikanin matakai domin kawar da matsalolin da mata tsofaffi suke fuskantar. (Jamila)