logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Kano ta fara tura dalubai 501 zuwa kasashen waje domin karo karatu

2023-07-01 14:50:21 CMG HAUSA

 

Zuwa karshen wannan shekarar ta 2023 gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya za ta tura dalabai ’yan asalin jihar zuwa kasashen waje, ciki har da kasar Sin domin karo karatu.

Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya tabbatar da hakan jiya Juma’a 30 ga watan Yuni a gidan gwamnatin jihar yayin da yake karbar bakuncin mai martaba sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero lokaci da ya kai masa ziyarar barka da salla wadda ake yiwa lakabi da Hawan Nasarawa a cigaba da shagulgulan bikin salla da ake gudanarwa a jihar wanda jiya aka shiga rana ta uku.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.