logo

HAUSA

Jakadar Sin a Nijar ya gana da ministan harkokin wajen kasar

2023-07-01 21:08:11 CMG Hausa

A ranar 30 ga watan Yuni ne, jakadan kasar Sin a Nijar Jiang Feng ya gana da ministan harkokin wajen Nijar Hassoumi Massoudou. Bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi kan alakar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu.

Jakada Jiang ya bayyana cewa, amincewa da juna ta fuskar siyasa a tsakanin kasashen biyu na kara zurfafa, kuma hadin gwiwa na ci gaba da bunkasa a aikace. Ba da dadewa ba, an yi nasarar gudanar da dandalin zuba jari na kasar Sin da Nijar karo na farko a Nijar. Kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga bin diddigin aiwatar da sakamakon dandalin, da ba da gudummawa ga ci gaban harkokin tattalin arziki da zamantakewar kasar Nijar.

Ministan harkokin wajen Nijar Hassoumi ya yabawa dandalin zuba jari matuka, inda ya bayyana cewa, kasar Nijar na mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana son karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban da kasar Sin, domin amfanar jama'ar kasashen biyu. (Yahaya)