logo

HAUSA

Sin: Ya dace Amurka ta ingiza hada kan UNESCO bayan dawowarta hukumar

2023-07-01 15:45:49 CMG Hausa

Jiya Juma’a 30 ga watan Yuni, an zartas da wani daftarin kuduri yayin taron musamman na babban taron UNESCO wato hukumar kula da ba da ilmi da kimiyya da al’ada ta MDD, inda aka amince da maido da matsayin mambar kasar Amurka a hukumar tun daga watan Yulin da ake ciki daga duk fannoni. Daga baya zaunannen wakilin kasar Sin dake hukumar Yang Jin ya jaddada cewa, bayan dawowar Amurka hukumar, ya dace ta yi kokari domin ingiza hada kan hukumar, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen mambobin hukumar, a maimakon raba kai ko kawo baraka.

Yang Jin ya kara da cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta cika alkawarin da ta dauka, ta sauke nauyin dake bisa wuyanta, kuma ta biya kudin haraji a kan lokaci, tare kuma da biyar daukacin kudin haraji da ba ta biya a cikin ‘yan shekarun da suka gabata ba a kan lokaci.

Bisa kudurin da aka zartas da shi, Amurka za ta biya kudin haraji da hukumar take binta a kai a kai, a sa’i daya kuma, za ta samar da tallafin kudi ga hukumar domin gudanar da ayyukan dake shafar tsaron lafiyar manema labarai da ba da ilmi a kasashen Afirka. Rahotannin da kafofin watsa labarai suka gabatar sun nuna cewa, gaba daya adadin kudin da hukumar UNESCO take binta ya riga ya kai dalar Amurka miliyan 619.

An labarta cewa, Amurka ta taba janye jiki daga hukumar sau biyu wato a shekarar 1984 da kuma ta 2018, lamarin da ya gamu da suka daga kasa da kasa. (Jamila)