logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya tsayar da kudurin daina aikin MINUSMA

2023-07-01 16:13:24 CMG Hausa

A jiya Juma’a 30 ga watan Yuni ne kwamitin sulhun MDD ya zartas da wani kuduri, inda ya tsayar da kudurin daina aikin tawagar kiyaye zaman lafiya ta majalisar a kasar Mali wato MINUSMA a takaice, kudurin ya fara aiki ne nan take.

Kwamitin sulhun ya yaba da kokarin da tawagar take yi a cikin shekaru goma da suka gabata, kuma ya yi maraba ga gwamnatin wucin gadi ta kasar Mali da ta cika alkawarin da ta yi wato ta yi babban zaben kasar a shekarar 2024 mai zuwa cikin ‘yanci kuma bisa adalci. A cikin kudurin da aka zartas da shi, kwamitin sulhun ya bukaci tawagar da ta daina gudanar da aiki tun daga yau ranar 1 ga watan Yuli, ta mika aiki tare kuma da janye jiki daga kasar nan da ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2023.

An kafa tawagar MINUSMA ne a watan Afililun shekarar 2013. (Jamila)