logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a samar da yanayin shawo kan rikicin Ukraine baki daya

2023-06-30 19:15:50 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki da su samar da yanayin da ya dace na warware rikicin Ukraine baki daya.

Geng Shuang ya bayyana haka ne yayin wani taron kwamitin sulhu na MDD game da samar da makamai ga Ukraine.

A cewarsa, bisa la’akari da yanayin da ake ciki yanzu, duniya na bukatar dakatar da yaki maimakon samar da makamai, da tattaunawa maimakon ta’azzarar rikici, da kuma tattaunawar zaman lafiya maimakon fito na fito tsakanin kungiyoyin kasashe. (Fa’iza Mustapha)