logo

HAUSA

Sudan ta yi Allah wadai da kona Alkur’ani mai tsarki a Sweden

2023-06-30 11:40:53 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta yi matukar Allah wadai da kona Alkur’ani mai tsarki da wani mai zanga-zanga ya yi a birnin Stockholm na kasar Sweden, matakin da a cewar ma’aikatar, muzantawa ne, da kuma tsokanar daukacin musulmin duniya.

Rahotanni sun ce a ranar babbar sallah, wani dan kasar Sweden mai asali daga Iraqi, ya yaga kwafin alkur’ani mai tsarki, kana ya kona shi a gaban wani masallaci dake birnin Stockholm, yayin da ake tsaka da gudanar da wata zanga-zanga da mahukuntan Sweden din suka ba da damar aiwatarwa, lamarin da ya yi matukar harzuka al’ummun kasashen Larabawa, da ma daukacin musulmin duniya. 

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta bayyana matukar damuwa game da maimaituwar irin wannan cin zarafi ta hanyar kona Alkur’ani mai tsarki, wanda laifi ne na keta alfarmar addinai. Tana mai jaddada adawarta ga duk wani mataki na nuna kyamar addinai.

Daga nan sai ma’aikatar ta yi kira ga dukkanin sassa, da su rungumi akidun kai zuciya nesa, da amincewar juna, da zaman lafiya, da jituwa tsakanin dukkanin al’ummun duniya.   (Saminu Alhassan)