logo

HAUSA

AUEOM: An gudanar da zaben Saliyo cikin kwanciyaer hankali da lumana

2023-06-30 11:40:10 CMG Hausa

Tawagar kungiyar Tarayyar Afirka (AUEOM) da ta sanya ido kan yadda aka gudanar da zabuka a kasar Saliyo ta bayyana cewa, an gudanar da babban zaben kasar na ranar 24 ga watan Yuni cikin kwanciyar hankali da lumana.

Tawagar ta yabawa al'ummar Saliyo, kan yadda suka nuna himma da jajircewa wajen bayyana ra'ayinsu a rumfunan zabe da kuma jajircewarsu na tabbatar da dorewar mulkin demokuradiyya.

A ranar Talatar da ta gabata ce, hukumar zaben kasar ta ayyana shugaban kasar mai ci kuma dan takarar jam'iyyar SLPP mai mulkin kasar Julius Maada Bio, a mtasayin wanda ya lashe wa'adinsa na biyu na shekaru biyar a zaben shugaban kasar na bana. (Ibrahim Yaya)