logo

HAUSA

Habasha na neman shiga BRICS

2023-06-30 20:47:19 CMG HAUSA

Jiya Alhamis, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Habasha Meles Alem ya shedawa manema labarai cewa, kasar na mika takardar neman shiga kungiyar BRICS.

BRICS, kungiyar kasashe ce masu samun saurin ci gaba da suka hada da Sin da Rasha da Indiya da Brazil da Afrika ta kudu. An ba da labari cewa, kasashen da suke neman shiga wannan tsari kwanan baya sun hadda da Bangladesh da Masar da Iran da Argentina da Saudi Arabia da hadaddiyar daular Larabawa da kuma Nigeria. (Amina Xu)