logo

HAUSA

Sarakuna a jihar Katsina sun nuna damuwa kan yadda har yanzu ake fuskantar matsalar tsaro a jihar

2023-06-30 09:42:39 CMG Hausa

Mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya bukaci gwamnati da ta kara bullo da wasu sabbin matakai da za su kawo karshen kalubalen tsaro a jihar, wanda ya yi sanadin tabarbarewar harkokin walwala da kasuwanci.

Sarkin ya bukaci hakan ne jiya Alhamis yayin hawan Bariki da masarautar Katsina ta saba gudanarwa a duk lokacin bikin babbar Sallah, inda sarkin ke kai ziyarar barka da salla ga gwamnan jihar a gidan gwamnati.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mai martaba sarkin na Katsina ya ci gaba da cewa jihar ta Katsina wadda take da tarihin zaman lafiya a arewacin Najeriya, yanzu kuma ta koma yankin da rayukan jama’a ke cikin barazana, a don haka lokaci ya yi da ya kamata a sami fahimta tsakanin al’umma da jami’an tsaro domin dai yakar ’yan ta’addan da suka hana dorewar zaman lafiya a jihar baki daya.

“Jinin mutum ya zama kamar a bude fanfano ruwa ya rinka zuba, kullum haka ake ta kashe al’umma ta, a karon farko ni kaina sai da na sallaci gawarwakin mutum 18 abun da ban taba yi a rayuwata, kaso 90 na masu aikata wannan ta’addancin masu shan kwaya ne, duk mai hankali ba zai aikata wannan aika-aika ba, a don haka mai girma mataimakin gwamna ina kira ga gwamnati ta kara mikewa tsaye sosai domin yiwa tufkar hanci ba wai kawai a jihar Katsina ba har da sauran sassan Najeriya.”

A jawabin da ya gabatar, gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umar Radda wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Alhaji Faruk Lawal Jobe ya tabbatar da cewa  gwamnati mai ci yanzu za ta hada hannu da masu rike da sarautun gargagjiya domin daidaita al’amuran tsaro a jihar ta Katsina.

Ya tabbatarwa sarkin cewa yanzu haka gwamnati na shirin daukar matasa ayyukan tsaro musamman ma matasan dake daf da garuruwan da aka fi samu hare-haren ’yan ta’adda.

Mataimakin gwamnan na jihar Katsina ya kuma kara dacewa, “Yau kwana 30 ke nan da shigar ofis mun yi tsare-tsare da dama da sauran shugabannin hukumomin tsaro dake jihar Katsina kamar kwamashinan ’yan sanda, daraktan tsaro na DSS da na Civil Defence da shugabannin sojojin sama da kasa da suke a jihar Katsina, inda muka yi taro da su muka nemi su hada kan su tare da baiwa gwamnatin jihar goyon baya, muka kuma bukaci cewa su kawo mana tsari da suke neman taimakon gwamnatin jihar, kari ke nan a kan wanda gwamnatin tarayya ke ba su domin dai talaka ya samu tsaro a jihar ta katsina.”

Shi dai wannan hawan Bariki an fara gudanar da shi tun a 1906 a birnin Katsina zamanin sarki Muhammadu Dikko, kuma ana gudanar da hawan ne kwana daya ga sallah inda a wancan lokaci sarki ke kai ziyarar barka da salla ga Baturen dake kula da lardin na Katsina. (Garba Abdullahi Bagwai)