logo

HAUSA

Shugaba Xi zai halarci taron SCO ta kafar bidiyo

2023-06-30 11:36:32 CMG Hausa

Bisa gayyatar da firaministan kasar Indiya Narendra Modi ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron dandalin kawance na Shanghai ko SCO karo na 23.

A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, shugaba Xi zai halarci taron wanda zai gudana a ranar 4 ga watan Yuli mai zuwa ne ta kafar bidiyo daga birnin Beijing, zai kuma gabatar da muhimmin jawabi.  (Saminu Alhassan)