logo

HAUSA

Babban jami’in diflomasiyar Sin ya gana da mataimakiyar babban sakataren MDD

2023-06-30 11:38:17 CMG Hausa

Darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS Wang Yi, ya gana da mataimakiyar babban sakataren MDD Amina Mohammed a birnin Beijing, fadar mukin kasar Sin.

Wang wanda har ila yau mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya ce, a mtasayinta na mamba, kasar Sin tana goyon bayan manufar MDD. Kuma a ko da yaushe kasar Sin za ta kasance mai kokarin samar da zaman lafiya da gudummawa ga ci gaban duniya, kana mai kare tsarin kasa da kasa, ba tare da la'akari da inda kasar Sin take a tarihi ko wane irin mataki na ci gaba ta kai ba.

A nata jawabi Amina Mohammed ta godewa kasar Sin, kan yadda take goyon bayan MDD, tana mai cewa, bangarorin biyu sun gudanar da hadin gwiwa mai zurfi a fannonin kiyaye zaman lafiya da bunkasuwa.

Ta bayyana cewa, MDD ta yaba tare da goyon bayan muhimman tsare-tsare da kasar Sin ta fito da su, kamar shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma shirin raya duniya. Ta ce, a yayin da duniya ke fuskantar kalubale da dama, wajibi ne mu tsaya tsayin daka kan hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, da neman jagorancin kasar Sin don samar da mafita tare. (Ibrahim Yaya)