logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi fashin baki game da matsayar kasar sa don gane da bukatar hadin kan kasa da kasa a fannin kare hakkin bil adama

2023-06-29 11:22:30 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD da sauran hukumomin kasa da kasa dake birnin Geneva na kasar Switzerland, ya jaddada matsayar kasar Sin don gane da bukatar gudanar da hadin kai a fannin kare hakkin bil adama.

Ambasada Chen Xu, wanda ya yi tsokacin yayin taro na 53 da ya gudana a jiya Laraba, ya ce tun shekaru 30 da suka gabata ne dandalin taron kare hakkokin bil adama na MDD ya amince da yarjejeniyar Vienna, da shirin aiki mai nasaba da hakan, kana aka amince da yin aiki tukuru domin karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, wajen ganin an cimma nasarori masu ma’ana a fannin kare hakkokin bil adama.

Kaza lika a cewar sa, kasar Sin bata taba yin kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ba da cikakken goyon baya ga hadin kan sassan kasa da kasa, da ingiza manufar gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama, da yunkurin gina duniya mai yalwa tare. (Mai fassara: Saminu Alhassan)