logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Kano za ta fitar da manufofi masu alaka da batutuwan kiwon lafiya, ilimi, noma da sha’anin tsaro

2023-06-29 10:07:50 CMG Hausa

Gwamnan jihar Kano na Najeriya Injiniya Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da aniyar gwamnatin jihar na inganta sha’anin kiwon lafiya, da noma da ilimi, tsaftar muhalli, samar da ingantaccen tsaro da ayyukan yi ga mata da matasa.

Ya bayyana hakan ne jiya Laraba jim kadan da kammala sallar idi da aka gudanar a babban masallacin idi dake cikin birnin Kano.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce, hakika gwamnati ta lura da matsalolin da al’ummar jihar ke ciki, a saboda haka za a yi duk mai yiwuwa wajen warware su sannu a hankali.

“A madadin gwamnatin jihar Kano ina taya al’umma murna ranar zagayowar babbar sallah na wannan shekara 10 ga watan zulhijja dai dai da 28 ga watan Yunin 2023 tare da fatan za a gudanar da bukukuwan sallah lafiya tare da fatan Allah ya dawo da alhazai gida lafiya.”

Shi ma mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a sakonsa na barka da sallah ya yi addu’ar samun damuna  mai albarka sannan ya yi kira ga gwamnati kamar haka.

“Muna kuma kira ga gwamnati ta ci gaba da taimakawa manomanmu da shawarwari kan yadda noma zai habaka da samar da ingantaccen iri da takin zamani ga manomanmu, sannan ya bukaci jama’a da su ci gaba lura da magudanan ruwa kasancewa akwai alamun ruwan mai yawa a damunar bana.”

Wasu daga cikin mazauna birnin Kano sun gabatar da sakonsu na sallah ga ’yan uwa da abokan arziki.

Hafsa Abdullahi Musa daga karamar hukumar Ungogo a jihar Kano da Alhaji Abdullahi Idirs Zuciya Shugaban ’yan kasuwan janmhuriyar Nijar dake Najeriya da kuma Isa Ibrahim dan kasar Chadi dake zaune a jihar Kano na daga cikin mutanen da suka zanta da CRI inda dukkanninsu suka yi fata alheri ga ’yan uwa da abokan arziki tare da addu’ar dorewar zaman lafiya a kasashensu.

(Muryar daga Hafsa Abdullahi Musa + Alhaji Abdullahi Idirs Zuciya+ Isa Ibrahim) 

(Garba Abdullahi Bagwai)